• Breaking News

  Sunday, November 22, 2015

  Darasi akan sallar asuba.
  Assalamu Alaikum yan uwa musulmai.
  Kowa yasan cewa sallar asuba tanada muhimmanci sosai ga tsagwaron lada mai tarin yawa sosai ga falala ga kuma jin dadi, abinda nake nufi da jin dadi shine duk wanda yatashi yayi sallah cikin lokacin ta musamman sallar asuba zaiji wani irin dadi a ransa kuma zaiji kamar an safke masa wani nauhi babba a kansa duk da cewar Manzon Allah SAW ya umaurci da kada mutum ya koma barci ya cigaba da lazimi, hailala, salati, karatun kurani da sauransu. Bisa wannan ne na dan tsakuro wani labari mai matukar ban dariya da zaisa muhankalta mudunga tashi da kuma yin sallar asuba cikin lokaci don Allah batare da wani dalili ba.

  Wani masallacine babba a wata unguwa, sai liman ya lura mutanen unguwar basu kaunar fitowa sallar asuba, sai azo sallar asuba baifi sahu daya ba. Sai liman ya shirya huduba mai ban sha'awa ranar Juma'a saboda mata na yawan halartar sallar. Liman yace "mata su riqa tada mazansu domin zowa sallar asuba, wadda duk ba'aganin mijinta masallaci,to kwamitin masallaci zai biyawa mijinta sadaki, a kara mai mata" a subar ranar asabar saiga masallaci ya cika har waje. Wata matar saida ta kawo mijin har bakin masallaci sannan ta koma.


  Allah yasa mudunga daurewa mutashi muyi sallar kuma mudunga koyawa iyalanmu kuma da karfafa musu gwiwa da su daurea Ameen.
  Allah yasa mu dace ameen.

  No comments:

  Post a Comment