• Breaking News

  Sunday, July 3, 2016

  Bikin Sallah: Akwai Yiwuwar Kai Harin Ta'addanci A Masallatai -DSS


  Hukumar tsaro na farin kaya wato DSS ta tabbatar da cewa tana da bayanan sirri da ke nuna cewa akwai miyagu da suka shirya kai jerin hare haren Ta'addanci a masallatai a lokacin bikin sallah da ake sa ran yi a ranar Talata mai zuwa.
  Da yake karin haske a kan batun, Mai Magana da yawun hukumar ta DSS, Mista Tony Opuiyo ya gargadi al'ummar Nijeriya ka su guji wasu abubuwa da ba su amince da su ba tare kuma da kai rahoton duk wanda ba su yarda da shi yana mai cewa bayanan sirrin sun kuma nuna cewa a shirya kai hare haren a wuraren shaktatawa.

  No comments:

  Post a Comment