• Breaking News

  Sunday, July 3, 2016

  Mu Marawa Buhari Baya Don Ganin An Dawo Da Martabar Kasar Nan, Sakon Gwamna Ganduje Ga Al'ummar Nijeriya


  Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga al'ummar Nijeriya da su marawa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari baya don ganin an dawo da martabar kasar nan
  Gwamnan ya kara da cewa duk da matsalar tattalin arziki da sauran matsalolin da sabuwar gwamnatin ta gada amma hakan bai sa shugaba Buhari ya yi kasa a gwuiwa ba a kokarin da yake na ganin kasar ta zama abar alfahri ga al'ummarta.
  Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin bude bakin da fadar gwamnatin jihar Kano ta shiryawa membobin kwamitin dattawan jam'iyyar APC da wasu jigogin jam'iyyar a fadar gwamnatin jihar.
  "Kasancewar gwamnatin Buhari tana tuhumar wadanda suka ci kudin sayen makamai, hakan ya nuna cewa gwamanti na kokarin ganin ta kawar da rashawa.
  “Haka kuma cikin shekara guda mun ga irin rawar ganin da gwamnati ta taka wajen dawo da harkar tsaro wanda a dalilin haka an dakile 'yan Boko Haram a jihohin Borno, Adamawa, Yobe har ma da Gombe", inji gwamnan.
  Don haka gwamna Ganduje ya yi kira ga al'ummar Nijeriya da su baiwa gwamnatin APC hadin kai kuma su yi mata addu'a don ganin shugaba Buhari ya cimma kyawawan kudirorin da yake da su kan kasar nan.

  No comments:

  Post a Comment