• Breaking News

  Sunday, July 3, 2016

  Ya Dabawa Kishiyar Mahaifiyarsa Wuka A Ciki

  A jiya Juma'a ne da misalin karfe sha daya na safe wani matashi dan kimanin shekaru 19 zuwa 20 me suna Sulaiman (Manu) ya caka wa kishiyar mahaifiyar sa mai suna Hajiya Amina wuka a ciki.
  Lamarin wanda ya auku a kan Layin Wunti bayan filin kwallo dake garin Bauchi a gidan Alhaji Audu Danbaba, bincike ya nuna cewa rikicin ya samo asali ne sakamakon cacar baki da ya shiga tsakanin Malama Maryam wato mahaifiyar Sulaiman (manu) da kishiyar ta Hajiya Amina akan yin kunun shan ruwa.
  Inda bayan cacar bakin ya ki karewa hakan ya sa Sulaiman dake cikin daki ya fito saboda bacin rai da zuciya ya cakka mata wuka a ciki saboda munanan kalaman da ya ji kishiyar mahaifiyar tasa na gaya mata.
  Yanzu dai an garzaya da Hajiya Amina asibiti, inda shi kuma Manu 'yan sanda suna neman sa ruwa a jallo.

  No comments:

  Post a Comment